'Yan majalisar Jigawa sun kaddamar da shirin mayar da yaran da basa zuwa makaranta azuzuwa

'Yan majalisar Jigawa sun kaddamar da shirin mayar da yaran da basa zuwa makaranta azuzuwa

Mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar dake wakiltar mazabar Gumel, Isyaku Abubakar ya shaidawa manema labarai cewar shi da takwarorinsa sun dauki raskwanar yaran da basa zuwa makaranta a yankunan su kuma sun kaddamar da shirin kai su makarantu domin samun ilimi.

Abubakar ya bayyana cewar tuni ya kai yara 1,800 makaranta tare da basu rigar makaranta da jakar saka litattafai da 'dan kudin tara domin karfafa musu gwuiwar samun ilimin.

Yayin kaddamar da shirin wanda ke samun goyan bayan Hukumar UNICEF, mataimakin shugaban majalisar ya ce a mazabarsa ya gano irin wadannan yara 4,000, kuma ya yi nasarar rajistar 1,800 domin fara karatun.

'Dan majalisar ya ce za suyi kokarin tabbatar da dorewar shirin wajen sanya tallafi kamar yadda tsarin gwamnatin jihar ya tanada.

Shi ma 'dan majalisar dake wakilatar mazabar Hadejia Abubakar Jallo ya ce sun gano irin wadannan yara akalla 2,200 a mazabar sa, kuma an saka su a makaranta.

Alkaluman hukuma sun bayyana cewar akalla yara sama da miliyan 20 basa zuwa makaranta a Najeriya, kuma akasarin su sun fito ne daga yankin arewacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)