A Najeriyar,kungiyoyin farar hula kusan ashirin ne suka bayyana damuwa a kai yan lokuta bayan wannan taro da ya gudana a Abuja.
Tun a shekarun 1990, da zanga-zangar adawa da aikin hako da kuma gina bututun mai na Shell, an daina hako mai daga yankin Ogoni.
Wasu yankunan Ogoni a Najeriya AP Photo/Sunday AlambaAn dade ana samun alamun samun sauki, in ji Alex Sewell, kwararre a yankin Niger Delta.
Amma ya lura da yadda tsarin ke kara habaka: “A cikin watan Disamba, gwamnati ta amince da sayar da wuraren mallakar Shell ga wata hadakar Najeriya. Alex Sewell na cewa ya yi imanin cewa wannan tattaunawa game da sake dawowa da hako mai a wannan yanki ya fito ne daga wannan yarjejeniya.
Wasu masu zanga-zanga a Najeriya. AFP PHOTOA cikin wata sanarwa, sun jera bukatu 14. Celestine Akpobari, shugabar Cibiyar Ci gaban Jama'a da masu kare hakkin muhalli. “Ya kamata shugaban kasar Najeriya ya dakatar da duk wani shiri na ci gaba da hakar ma’adanai a filayen Ogoni har sai an samu tuntuba mai ma’ana da al’ummar Ogoni a bangarori da suka jibanci muhalli da rayuwar jama’a.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI