Ƙwararrun a fannin haɓakar tattalin arziƙin ƙasashe a asusun IMF reshen Afrika da suka ƙunshi Athene Laws da Fathen Saliba sun ce akwai buƙatar ɗaukar matakan gaggawa kan abin da ya shafi rashin aikin yi tsakanin ƙasashen Afrika, musamman waɗanda ke fama da ƙarancin kuɗaɗen shiga.
Ƙwararrun waɗanda suka yi musayar bayanai da ra’ayoyi yayin taron haɗaka tsakanin IMF da World Bank da ke gudana a birnin Washington na Amurka, sun ce babbar matsalar nahiyar Afrika bai wuce rashin samar da guraben ayyuka ba, ta yadda hatta matasan da suka yi dogon karatu kan ɓige da zaman kashe wando.
Ƙwararrun sun ce ƙasashen na Afrika da Najeriya akan gaba na buƙatar aiwatar da abubuwa guda 3 gabanin samar da gobe mai kyau ga matasansu, ciki kuwa har da sauya fasalin kasuwanci marasa rijista da bunƙasa tsare-tsaren da za su haifar da ci gaba baya ga magance matsalolin rashin bunƙasar kamfanoni masu zaman kansu.
A cewar ƙwararrun gaza samar da guraben ayyukan yi, da ake ganin a ƙasashen na Afrika su ke shafe goben al’ummomin wannan yanki tare da haddasawa ƙasashen mummunan koma baya ta fuskar tattalin arziƙi wanda ke haifar da tarin matsaloli.
IMF da bankin duniya sun bayyana yadda kamfanoni masu zaman kansu ke ci gaba da fuskantar koma baya a ƙasashen Afrika, ta yadda hukumomi da ma’aikatun gwamnati kaɗai kan iya samar da guraben aiki masu gwaɓi.
A cewar hukumomin kuɗin biyu, gwamnatocin na Afrika baza su iya wadata al’ummominsu da ayyuka ba, wanda ke nuna cewa wajibi ne haɗa hannu wajen haɓaka kamfanoni masu zaman kansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI