Shugaban ƙungiyar mai barin gado Yakubu Mai Kyau ya ce abin baƙin ciki ne yadda Dangote ke fuskantar zagon ƙasa daga bangarori da dama wajen ganin matatar ta fara aiki gadan gadan.
Mai Kyau ya zargi masu shigo da mai ƙasar waɗanda suka hana Najeriya tace mai a gida da haifar da tarnakin da ya hana sabuwar matatar aikin tace man da zai hana ƙasar shigo da shi daga ƙasashen ƙetare.
Shugaban wanda ya jagoranci tawagar muƙarrabansa domin ziyarar gani da a ido matatar dake unguwar Lekki a Lagos, ya ce abinda ya gani ya faranta masa rai matuka, yayin da ya bayyana Aliko Dangote a matsayin mai fafutukar ƴantar da jama'a kuma gwarzo saboda sadaukar da ran da ya yi wajen zuba jarin dala biliyan 20 domin samar da matatar.
Mai Kyau ya buƙaci gwamnatin Najeriya ta gaggauta samar da yanayi mai kyau ta yadda wannan matatar zata fara aiki gadan gadan domin ragewa Najeriya wahalar da ta ke sha na samun tacaccen man.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI