Ya kamata a kiyayi sayen ƙuri'u a lokutan zaɓe a Najeriya - Abdulsalam Abubakar

Ya kamata a kiyayi sayen ƙuri'u a lokutan zaɓe a Najeriya - Abdulsalam Abubakar

Abdulsalami, wanda shine shugaban kwamitin wanzar da zaman lafiya na ƙasa NPC, ya yi wannan kira ne a wurin taron rattaba hanu kan yarjejeniyar lumana a lokacin zaben gwamna a jihar Ondo wanda zai gudana a ranar 16 ga watan Nuwamba da muke ciki.

Taron da ya gudana a Akure babban birnin jihar a ranar juma’a ya samu halartar ƴan takarar jam’iyun siyasa 17 da zasu fafata in a lokacin zaɓen.

Sannan Abdulsalam ya kirayi ƴan takarar  da su kasance masu rungumar ƙaddara wajen la'akari da duk yadda sakamakon zaben zai kasance.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)