Wasu tubabbun mayaƙan boko haram da ke taimakawa Sojin Najeriya sun tsere

Wasu tubabbun mayaƙan boko haram da ke taimakawa Sojin Najeriya sun tsere

Jaridar Premium Times da ake wallafawa a Najeriyar ta ruwaito cewa mayaƙan 13 na daga cikin ɗaruruwan mutanen da suka aje makaman su tare da gabatar da kansu ga hukumomin tsaro.

Wani mai bincike a Najeriyar Samuel Malik ya shaidawa jaridar cewar tubabbun mayakan 13 na yaƙi ne tare da sojoji a ƙaramar hukumar Mafa da ke jihar Borno kafin tserewar da suka yi a watan jiya.

Jami'in ya ce bayan tserewarsu sun naɗi bidiyo inda suke nuna makaman da suka tsere da su.

Tun bayan da Sojin Najeriya suka fara nasarar murƙushe ƴan ta'addan na Boko Haram a shekarar 2015 ne aka fara ganin yadda mayaƙan ke ajje makamansu tare da miƙa wuya ga mahukuntan ƙasar wanda ya bayar da damar horar da su don sauya musu ɗabi'u yayinda aka sanya wasu a cikin runduna ta musamman don taimakawa dakarun ƙasar wajen murƙushe barazanar tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)