Wani Sufeton 'yan sandan Najeriya ya harbe wani mawaki Okezie Mba

Wani Sufeton 'yan sandan Najeriya ya harbe wani mawaki Okezie Mba

 

Rahotani daga yankin na bayyana cewa sufeto dauke da makami ya harbi  mawakin Okezie Mba wanda aka nan da nan aka garzaya da shi asibiti, inda likitan da ke kula ya tabbatar da mutuwarsa. An ajiye gawarsa a dakin ajiyar gawarwaki na yankin.

Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu ta tabbatar da faruwar lamarin.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Enugu, Daniel Ndukwe ya fitar a yau asabar, ya ce an kama jami’in da kuma tsare shi da laifin kashe mawakin.

Wani ruƙuni na ƴan sandan Najeriya. Wani ruƙuni na ƴan sandan Najeriya. AP - Sunday Alamba

Sai dai kakakin ya ce jami’in dan sandan namiji ne da ke aiki a sashin yaki da cin hanci da rashawa na ‘yan sanda a jihar Enugu.

"An ba da rahoton cewa mawakin yana barin hedikwatar Squad bayan ziyarar sada zumunci, inda, saboda dalilan da har yanzu ba a tantance ba, dan sandan ya harba bindigarsa kan mawakin.

Daniel Ndukwe ya ce kwamishinan ‘yan sanda a jihar Enugu, Kanayo Uzuegbu, ya umarci mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da ke kula da sashen binciken manyan laifuka na jihar ya binciki lamarin.

'Yan Sandan Najeriya 'Yan Sandan Najeriya AP - Sunday Alamba

Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Enugu ya jajanta wa iyalan mawakin kuma ya bayyana mutuwarsa a matsayin "abin takaici ne kuma ba za a yarda da shi ba."

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)