Rahotanni sun ce cutar ta ɓarke a ƙananan hukumomi 3 na jihar, kuma zuwa yanzu an sami rahoton mutane 1,160 da cutar ta kama.
Kwamishiniyar Lafiya ta jihar Asabe Balarabe, ce ta bayyana hakan lokacin da take zantawa da manema labarai.
Kwamishiniyar ta kuma yi ƙarin hasken cewa zuwa yanzu ana kan kula da mutane 15 a da ke kwance a asibiti, waɗanda suka fito daga ƙanana hukumomin Sokoto ta arewa da Silame da kuma Kware.
Bayanai sun nuna cewa tuni jama’a suka fara tururuwar zuwa ɗakunan gwajin lafiya musamman mata masu juna biyu da kuma ƙananan yara, matakin da kwamishiniyar ta yaba da shi ƙwarai da gaske.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI