Wani harin bata gari ya katse hasken lantarki a wasu yankunan Lokoja da Abuja

Wani harin bata gari ya katse hasken lantarki a wasu yankunan Lokoja da Abuja

Sanarwar da kamfanin ya fitar, ta bayyana cewa, ta'adin da aka yi wa turakun ya haifar da babban cikas ga aikin samar da wuta a yankuna da dama na jihar Kogi da yankin Gwagwalada da ke Abuja babban birnin kasar.

A baya-bayan nan ne yankin arewacin Najeriya ya kwashe akalla kwanaki 10 ba tare da samun wutar lantarki ba, sakamakon katsewar wutar da aka gani.

Wannan ya janyo wa 'yan kasuwa da dama asarar kayayyaki da kuma makudan kudade, musamman masu sana'ar sayen da danyen kifi da kuma dangogin nama, hadi da kayayyakin sanyi.

Shiga alamar sauti, domin sauraron rahoton Isma'il Karatu Abdullahi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)