Rahotanni sunce ƴan bindigar sun kewaye yankin da ke kan iyakar Kaduna da Niger da ƙarfe 12 na rana.
Bayanai sun ce ƴan bindigar sun kaɗa shanu tare da sace shagunan al’ummar yankin.
Jaridar Daily Trust ta rawaito wani shugaban al’ummar yankin wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce an tsinci gawar yarinyar ƴar shekara 7 a kusa da wani daji bayan ƴan bindigar sun tafi.
Ya ce ƴan bindigar sun kutsa ƙauyen ta wani gari mai suna Unguwar Mission domin su kai wannan hari. Ya ce a yayin harin an kashe mutum 2 tare da hallaka yarinya ƴar shekara 7.
Ƴan Bijilanti sun samu nasarar ƙwato shanun da a wani ƙauye dake Niger bayan kewaye ƴan bindgar da suka yi a dajin Uragi.
Shugaban Ƙungiyar Birnin Gwari Ishaq Usman Kasai ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai yi ƙarin bayani ba kan harin.
Jami’an ƴan sanda jihar Kaduna ba su ce komai ba dangane da harin da aka kai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI