Wani attajirin Afrika ta Kudu ya doke Ɗangote a kuɗi a yanzu

Wani attajirin Afrika ta Kudu ya doke Ɗangote a kuɗi a yanzu

Jaridar ta Bloomberg ta ce kuɗin attajirin Johann Rupert ya kai dala biliyan 1 da miliyan 87, yayin da na Ɗangote ke da dala biliyan 1 da miliyan 7.

Attajirin mai shekaru 74 shi ne mamallakin kamfanin samar da agogunan hannu na Cie Financiere Richmond da ke ƙasar Switzerland.

A nasa ɓangaren Aliko Ɗangote ɗan asalin Najeriya da ya kwashe shekaru da dama kan karagar wanda ya fi kowa kuɗi, yana da kaso 86 na kudinsa a kamfaninsa na siminti.

Ɗangote ya kuma samar da kamfanonin sarrafa siga, gishiri da sauransu.

Ƙari kan wannan kuma Ɗangote shi ne mamallakin sabuwar matatar man da aka samar da ke da ƙarfin tace ganga dubu 650 na danyen mai kowacce shekara.

Jaridar ta jero manyan attajiran nahiyar Afrika da suka fi kowa kudi guda biyar da suka hadar da Johann Rupert dan Afrika ta Kudu, da Nicky Oppenheimer dan Afrika ta Kudu sai Naseef Sawiris na masar da Natie Kirsh na Afrika ta kudu sai kuma Aliko Ɗangote na Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)