Waɗanda suka ɗauke Janar Tsiga sun buƙaci kuɗin-fansa na naira miliyan 250

Waɗanda suka ɗauke Janar Tsiga sun buƙaci kuɗin-fansa na naira miliyan 250

Wata majiya ta  da ke kusa da iyalansa, wadda ta buƙaci a sakaya sunanta ta ce lallai ƴan bindigan sun tuntuɓi lyalan, kuma sun nemi a basu kuɗin.

A cikin talatainin daren Larabar da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga da yawansu  ya kai dari suka kai farmaki gidan tsohon janar din da ke Tsiga, a ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina, su ka kuma yi awon gaba da shi tare da wasu mutane 9

Ya zuwa loakcin haɗa wannan rahoto, babu wata wani bayani daga kakakin sojin Birget na 17 da ke Katsina, ko kuma kakakin rundunar ‘yan sandan jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)