Shugaban sashen kula da bangaren abinci mai gina jiki na UNICEF dake Kano, Oluniyi Oyedokun ya bayyana haka lokacin da yake gabatar da jawabi wajen wani taron masu ruwa da tsaki kan inganta lafiyar mata masu juna biyu.
Jami'in ya ce daga cikin ko wadanne yara guda biyu da ka gani, dayan su na fama da wannan matsalar a Kano.
Oyedokun ya kara da cewar Gidauniyar Bill da Malinda na daukar nauyin shirin bada tallafi ga wadannan yara a jihohi 5 dake cin gajiyar sa cikin su harda Kano.
Jami'in ya kuma kara da cewar alkaluman hukuma sun nuna cewar kashi sama da 60 na matan dake yankin arewa maso yamma na fama da rashin kwayoyin halittar jinin dake sarrafa iska a cikin jinin su.
Oyedokun ya bayyana fatarsa na ganin jihar Kano ta zama ta farko da zata bada kudin karo karonta domin aiwatar da asusun tallafawa yaran da suke fuskantar matsalar rashin abinci mai gina jiki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI