Jami’ar sashin bai wa yara kariya ce Monica Aika ta bayyana haka a yayin bude wani taron masu ruwa da tsaki da aka shirya domin kawo karshen gallazawa kananan yara a Najeriya.
Jami’ar hukumar Monica Aiki ta bayyana cewa kusan kashi 6 cikin 10 na yara na fuskantar wani nau'i na cin zarafi, kuma kashi 5 cikin 100 ne kawai na wadanda suka bayar da wani bayani daya danganci aukuwar lamarin ke samun tallafi da kulawa.
A matsayin fargar jaji ga wannan binciken, Najeriya ta dauki matakai wajen karfafa gwiwar wadanda ke matukar kokari wajen kulawa da yaran da suka fuskanci matsalar da kuma kiyaye cin zarafinsu a nan gaba.
Ta kara da cewa sun yi kokari wajen tabbatuwar aiki cikin tsari da aiwatar da dokoki da kawar da dabi'un da ke karfafa wariyar jinsi da kuma ayyuka masu cutarwa kamar kaciyar mata da auren yara tare da samar da ingantaccen yanayi, hakazalika da kuma tallafawa iyaye da kuma masu ba da kulawa.
A nata jawabin, lauyar gwamnatin tarayya kuma babbar sakatariya a ma’aikatar shari’a ta Najeriya, Beatrice Jeddy-Agba, wadda ta ba da misali da binciken da hukumar kidaya ta kasa ta gudanar tun farko, ta ce kawo karshen cin zarafin kananan yara yana bukatar a bi matakai daban-daban tare da samun hadin kai.
Ita kuwa, daraktar hukumar kula da shari’ar manyan laifuka ACJRD a ma’aikatar shari’a ta kasar, Leticia Ayoola-Daniels cewa ta yi kasancewar taron share fage ne gabanin taron kolin duniya da za a yi a Bogota na kasar Colombia, zai bayar da damar duba irin ababen da suka kamata ayi wajen magance matsalar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI