Duk da yadda zanga-zangar da ta gudana a baya ta juye zuwa tarzoma tare da haddasa asarar ɗimbin rayuka musamman a jihohin arewacin Najeriyar, ƙungiyoyin yayin wani taronsu a jihar Lagos ta yankin kudanci, sun ce wajibi ne fita zanga-zangar a ranar 1 ga watan gobe na Oktoba wato ranar da ƙasar za ta bikin tunawa da ranar samun ƴanci.
A cewar ƙungiyoyin za su ci gaba da dawa da manufofin gwamnatin shugaba Bola Tinubu da suka ƙunshi janye tallafin man fetur tsaurara manufofin kuɗi da kuma hauhawar farashin kayaki.
Yayayin zanga-zangar watan jiya wadda aka yi wa laƙabi da #EndbadGovernanceinNigeria, an ga fitar dubban mutane a manyan biranen Najeriya, inda Amnesty International ke cewa mutane 21 suka mutu yayinda rundunar ƴan sandan ƙasar ta ce mutum 7 kaɗai suka mutu kuma jami’an tsaron ƙasar basu da hannu a kisan ko da mutum guda.
Sai dai duk da yadda ake ci gaba da tababa game da matsalolin da aka samu bayan waccan zanga-zanga, yayin wani taron manema labarai a Lagos shugabannin ƙungiyoyin irinsu Hassan Taiwo jagoran wata ƙungiya mai rajin tabbatar da daidaito a tsarin bayar da ilimi ya ce za su ɗora ne kan zanga-zangar da suka faro a watan na Agusta.
Masu zanga-zangar dai na neman lallai gwamnatin ƙasar ta rage farashin man fetur da na abinci baya ga lantarki da kuma sakin ilahirin masu zanga-zangar da aka kame a baya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI