Kungiyar ta ƙara bayyana matsayarta a wata sanarwa da ta fitar mai ɗauke da sa hannun shugaban kwamaitin gudanarwarta Al-amiin Daggash.
A cikin sanarwar NEF ta nuna damuwa kan yadda gyaran dokar zai iya cutar da yankin arewacin Najeriya da ma ƙasar baki ɗaya.
Ƙungiyar ta jaddada cewa ba wai ƴan Najeriya musamman yankin arewa na ƙalubalantar kawo dukkanin wani sauyi mai kyau da ma’ana daga hukumomin gwmanatin tarayya ko jihohi ko ƙananan hukumomi ba ne, illa kawai hanyoyin da aka bi wurin yin gyaran ya saɓa da yadda aka saba gani a sassan duniya.
Ta ƙara da cewa don haka akwai buƙatar samar da wani yanayi da za’a tattauna da masu ruwa da tsaki da kuma yin komai a buɗe tare da janyo kowa da kowa ta yadda gyaran zai dace da buƙatun alummar ƙasa.
Kungiyar dattawan Arewa ta ce sabuwar dokar harajin da gwamnatin Najeriya ta gabatar ya bayyana a fili cewar ta saɓa da dukkanin hanyoyin da aka saba ganin ana bi a faɗin duniya yayin da ake so a kawo sabbin tsare-tsare ko wasu ƙudurori na gwamnati
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI