UNESCO ta mika wa Najeriya shaidar karrama bikin hawan Sallar Kano

UNESCO ta mika wa Najeriya shaidar karrama bikin hawan Sallar Kano

Jakadiyar Najeriya a hukumar Ambasada Hajo Sani ce ta mikawa ministar al'adu Hajiya Hannatu Musawa takardar shaidar a madadin UNESCO lokacin da aka gudanar da wani kwarkwaryar biki a ofishinta dake Abuja.

Musawa ta bayyana matukar farin ciki dangane da wannan karramawar da UNESCO ta yiwa Najeriya a kan wadannan bukukuwa na Sallah dake janyo masu yawon bude ido daga kasashe daban daban na duniya.

Ministar ta bayyana aniyar gwamnatin Najeriya a karkashin Bola Ahmed Tinubu na inganta wadannan al'adu wadanda ke taimakawa wajen samar da gurabun ayyukan yi da kuma samun kudaden shiga.

Hawan Sallah a jihar Kano ta Dabo Tumbin Giwa dake arewacin Najeriya. 22 ga Fabarairu, 2002. Hawan Sallah a jihar Kano ta Dabo Tumbin Giwa dake arewacin Najeriya. 22 ga Fabarairu, 2002. AP - SAURABH DAS

Hajo Sani wadda ke wakilatar Najeriya a Hukumar UNESCO, ta bayyana bikin Hawan Dabar a matsayin wadda ke nuna irin ado da mutunci da kuma haɗin kan dake tsakanin al'umma mazauna birnin.

Ta ƙara da cewar bikin na da matuƙar girman da ke janyo ƙabilu daban daban domin gabatar da al'adun su ciki harda Hausawa da Fulani da Larabawa da Nufawa da Yarbawa da kuma Abzinawa waɗanda da dama daga cikinsu sun rikiɗe sun zama al'umma guda a birnin.

Bikin da ake gudanar da shi tun daga ƙarni na 15 ya haɗa da yadda Sarki ke jagorancin tawagar da ta ƙunshi hakimai da fadawa da kuma mahaya dawaki sama da 10,000 waɗanda suka ci ado ana kuma buga musu tambura da busa algaita akan wasu titunan birnin.

Waɗannan bukuwan dai ana yinsu ne sau biyu a shekara, wato bikin ƙaramar Sallah ko Eid el Fitr da babbar Sallah ko kuma Eid el Adha, a watan 10 na Shawwal da kuma Zul Hajj wato watan 12 na Islama.

Wani ɓangare na hawan Daba a jihar Kano a ranar biyu ga watan Fabarairun shekarar 2004. Wani ɓangare na hawan Daba a jihar Kano a ranar biyu ga watan Fabarairun shekarar 2004. ASSOCIATED PRESS - SAURABH DAS

Bikin da ake kira Hawan Daba na kuma gudana a birane da dama na Musulmi a ƙasar da Hausawa suka fi yawa a yankin arewacin ƙasar, sai dai hukumar UNESCO ta ce sun samo assali ne daga birnin Kano, birni na 2 mafi girma a Najeriya mai dauke da mutane sama da miliyan 4 a cikin ƙwaryarsa, kuma birni na 2 na shugaban addinin Islama mafi girma a ƙasar.

Shi dai wannan bikin Mai Martaba Sarkin Kano ke jagorancin sa tare da rakiyar hakimai da dagatai da fadawa waɗanda ke cin ado na fitar hankali domin bayyana irin farin cikin da suke ciki yi a wadannan ranaku masu matukar daraja ga al'ada da kuma addinin su.

Mai Martaba Sarkin Kano marigayi Alhaji Ado Bayero, yayin hawan Sallah a ranar 2 ga watan Fabarairun shekarar 2004. Mai Martaba Sarkin Kano marigayi Alhaji Ado Bayero, yayin hawan Sallah a ranar 2 ga watan Fabarairun shekarar 2004. ASSOCIATED PRESS - SAURABH DAS

Sarkin kan ratsa wasu titunan birnin Kano, yayin da jama'ar gari ke fitowa bakin titi suna miƙa gaisuwarsu tare da jinjinawa jagoransu.

Sai dai sauye sauyen da aka samu na mulki a halin yanzu sun rage karfin fada aji da sarakuna suke da shi a bangaren mulki, amma kuma suna da ƙarfin faɗa aji a tsakanin al’ummominsu waɗanda suka mayar da su a matsayin masu killace al’adu, abinda ke basu kima a tsakanin al’umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)