Wannan ya biyo bayan tattaunawa kan ƙudirorin da aka yi a zaman majalisar na yau Alhamis, wanda Sanata Opeyemi Bamidele mai wakiltar Ekiti ta tsakiya ya jagoranta.
Idan za’a iya tunawa dai a jiya Laraba ne wasu manyan jami’an gwamnatin Tinubu su ka hallara gaban majalisar tare da yin cikakken bayani game da ƙudurorin.
A zamanta na jiya, majalisar ta ƙi bai wa maganar Sanata Ali Ndume mai wakiltar kudancin Borno da Sanata Abdul Ningi da ke wakiltar Bauchi ta tsakiya, muhimmanci, waɗanda suka yi nuni da cewa bai kamata a bar wasu jami’an gwamnati su kare ƙudirorin harajin ba.
An samu hatsaniya a zauren majalisar kafin bai wa jami’an gwamnatin damar shigowa, domin ba’a sanya su a jerin ajandarsu ta ranar ba.
Shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ne dai ya buƙaci a yiwa dokar harajin garambawul, inda aka gabatar da sabbin ƙudurorin 4 a gaban majalisar, domin amincewa dasu, lamarin da ya janyo cece-kuce a ƙasar musamman a yankin Arewa.
Gwamnonin Arewacin ƙasar da shugabannin gargajiya da kungiyar datttawan Arewa sun yi watsi da wannan ƙuduri, domin a cewarsu ba’a bukatar wannan sauye-sauye a fannin harajin ƙasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI