Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar lauyan iyalan tsohon shugaban kasar Reuben Atabo ne ya bayyana haka ga manema labarai.
Sanarwar gwamnatin jihar Kaduna da Babban Daraktar ma'aikatar kula da filaye Mustapha Haruna ya gabatar tace Gwamna Sani ya rubutawa iyalan Janar Abacha wasika wanda aka sanya sunan Mohammed Sani Abacha da ta bayyana mayar musu da filayen da kuma gabatar musu da bukatar cewar su je su biya harajin da aka saba karba a hannun su na mallakar filayen.
A shekarar 2022 tsohon gwamnan jihar El Rufai ya gabatar da sanarwa a jarida a ranar 28 ga watan Afrilu wadda ta bayyana kwace filayen tare da soke takardun wadanda aka mallakawa.
Wannan mataki na tsohon gwamnan ya haifar da cece kuce sosai a ciki da wajen jihar Kaduna.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI