Tsohon gwamnan Kogi Bello ya gurfana a gaban hukumar EFCC

Tsohon gwamnan Kogi Bello ya gurfana a gaban hukumar EFCC

Wata sanarwar da mai taimaka masa a kan harkokin yada labarai Ohiare Michael ya gabatar, tace tsohon gwamnan ya samu rakiyar wasu fitattun mutane da kuma lauyoyinsa bayan tattaunawar da suka yi a tsakaninsu domin amsa tambayoyin da za'a masa.

A watan Afrilun da ta gabata, EFCC ta yi shelara neman tsohon gwamnan tare da tayin tukwuici ga duk wanda zai tsegunta mata inda za ta same shi domin amsa tambayoyi.

An ruwaito shugaban hukumar Ola Olukoyed na zargin tsohon gwamnan da aikata manyan laifuffuka da kuma kin amsa gayyatar da aka masa lokacin da yake ganawa da kafofin yada labarai.

Yunkurin kama shi da jami'an Hukumar DSS ta yi a gidansa dake Abuja ya gamu da cikas, sakamakon zargin kai masa daukin da aka yiwa gwamna mai ci Usman Ododo.

Daga cikin zarge zargen da ake masa harda halarta kudaden haramun da suka zarce naira biliyan 80 da miliyan 246, baya ga wasu dala dubu 720.

Kayode ya ce ya tattauna ta waya da tsohon gwamnan dangane da bukatar gabatar da kansa, amma sai ya ki amincewa, inda ya bukaci EFCC da ta je garinsu domin masa tambayoyin da take bukata.

Bello na daga cikin mutanen da suka nemi jam'iyyar APC ta gabatar da su  amatsayin 'yan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023 wanda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya lashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)