Tsoffin sojojin sun hallara a filin zanga-zangar da ƙarfe 7:30 na safiyar yau Alhamis ɗauke da tabarmin bacci da kujeru da kuma rumfar zama, inda suka zargi gwamnati da ƙin biyansu ƙarin kuɗin fansho na kashi 20 zuwa 28 cikin 100, daga watan Janairu zuwa Nuwambar shekarar 2024.
Rahotannni sun ce hakan na zuwa ne ƙasa da awanni 12 da wata ƙungiyar ƴan fansho ta gudanar da makamanciyar zanga-zangar domin neman a biya su haƙƙoƙinsu.
A jawabinsa ga manema labarai bayan rufe hanyar shiga ma’aikatar kuɗin Najeriya, Jagoran zanga-zangar Innocent Azubuike ya ce rashin biyan haƙƙoƙinsu ya jefa su cikin mawuyacin hali da bazai iya misaltawa ba.
Azubuike ya ce sun karkata akalar zanga-zangar zuwa ma’aikatar kuɗi maimakon ta tsaro ne saboda ma’aikatar tsaro ta kammala na ta aikin , domin ta amince a fitar musu da kuɗaɗensu.
A cewarsa suna buƙatar a biya su albashinsu da aka riƙe daga watan Oktoban 2023 zuwa Nuwambar 2024, da kuma ƙarin N32,000 a kuɗin fanshonsu, da kuma sauran manyan kuɗaɗe da ke ƙunshe cikin tanade-tanaden sallamar ma’aikatan soji.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI