Tsananin ya habaka cinikayyar barguna a Arewa maso Gabashin Najeriya

Tsananin ya habaka cinikayyar barguna a Arewa maso Gabashin Najeriya

A Kasuwar zamanin Jimeta, sanyi ya kawo babbar dama ga 'yan kasuwa, ta hanyar rubbanya cinikin barguna, safar hannu, da sauran tufafin sanyi.

Anas Dauda, mai sayar da gwanjo ne, ya bayyana yadda wannan kakar ke kawo sauyi a harkar kasuwancin sa.

" A irin wannan lokacin, gaskiya muna cinikin kayan sanyi sosai," in ji Anas

Sai dai, masana kiwon lafiya suna jan hankali game da tasirin sanyin na hunturu ga lafiyar jama'a, musamman masu fama da ciwukan da suka danganci numfashi kamar asma.

A yayin da 'yan kasuwa ke samun riba mai yawa daga wannan yanayi, alumma kuma na ganin cewar lokaci ne da ke bukatar shiri da kulawa ta musamman ga lafiyarsu.

Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken rahoton Ahmad Alhassan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)