Ministan Muhammad Idris ya ce shugaban Najeriya Bola Tinubu ya umarci ministan shari’a Lateef Fagbemi ya fara bin ƙa’idojin da doka ta tanada domin tabbatar da ganin an saki yaran.
Shugaban ƙasa ya umarci duk yaran da aka kama a sakesu sannan a haɗasu da iyalansu a duk inda suke a faɗin Najeriya. An kafa kwamiti da zai yi bincike kan ta yadda aka kama yaran tare d tsaresu. Dukkanin jami’an tsaron dake da alaƙa da kama yaran za a bincikesu kuma za su girbi abinda suka shuka
Umarnin da shugaba Tinubu kwanaki ƙalilan bayan zazzafar muhawarar da ta kaure a Najeriya bayan bayyanar hotuna da bidiyo na ƙananan yaran da aka kama tare da gurfanar da su a gaban kotu.
Ƙungiyoyi da masu ruwa da tsaki a ƙasar sun yi ta sukar kama yaran, galibinsu na ganin cewar yaran basu kai matsayin da za a gurfanar da su a gaban kotun ba.
Shafukan sada zumunta a ƙasar sun ɗauki dumi bayan bayyanar yaran cikin yanayi na yunwa da tsananin gajiya.
Wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta ya nuna yadda wasu daga cikin yaran suka yi ta faɗuwa lokacin da aka kaisu kotu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI