Daraktan yada labaran ma'aikatar tsaron Najeriya Henshaw Ogubike ya sanar da wannan umarnin sakamakon karuwar ta'addancin da wadannan 'yan bindiga ke yi a yankin.
Ogubike ya bayyana bacin ran gwamnati dangane da irin ta'addancin da aka gani a yankin arewa maso yammacin kasar, ya yin da yake cewa wannan umarni zai taimaka wajen tinkarar matsalar da kuma tabbatarwa jama'a gwamnati ta damu da halin da suke ciki.
A na shi tsokaci, minista Matawalle ya ce za su jagoranci aikin kawar da Bello Turji da tawagarsa daga yankin.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da wasu daga cikin 'yan ta'addan ke farfaganda da wani faifan bidiyo na kwace wata daga cikin motocin soji tare da konata a Kwashabawa dake karamar hukumar Zurmi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI