Shugaban, wanda kuma shine shugaban ƙungiyar ta ECOWAS a lokaci guda na jadadda wannan roƙo ne lokacin da yake ganawa da manyan hafsohin tsaron ƙasashe mambobin ECOWAS din a Abuja.
Ya ce babbar buƙatar ƙungiyar a yanzu shine dawo da ƙasashen cikin ECOWAS, la’akari da muhimmanci da suke da shi, musamman ta fannin tsaro.
A cewar sa, shugabancin Najeriya da kuma na ECOWAS a lokaci guda ya sanya jagorancin ƙungiyar ya kasance mai matuƙar tsauri a gareshi, don haka zai yi duk mai yiwuwa don ganin sun dawo cikin ƙungiyar ba tare da wani tashin hankali ba.
Shugaban na Najeriya ya gargadi ƙasashen kan cewa dagewar da suka yi na ƙin komawa ECOWAS ba zai haifar musu da komai ba illa koma baya, la’akari da cewa duk abinda za’a yi shi a ƙungiyance yafi armashi da kuma tasiri.
Daga nan kuma sai Tinubu ya yabawa shugabannin tsaron ƙasashe mambobin ECOWAS kan irin kwarewar aiki da suka nuna ta yadda har yanzu yaƙi bai barke tsakanin su da ƙasashen da suka yi iƙirarin ficewa daga ƙungiyar ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI