Aƙalla mutane 10 ne suka mutu, ciki har da ƙananan yara, yayin da da dama suka samu raunuku lokacin da jama’a suka taru domin ƙarban tallafin abinci a cocin Katolika da ke unguwar Maitama a Abuja babban birnin Najeriyar.
Hakazalika a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriyar, wasu mutane 29 suka mutu da dama suka jikkata a wani turmutsutsu a Okija, da ke ƙaramar hukumar Ihiala ta jihar.
To sai dai rundunar ƴan sandan jihar Anambra ta ce mutane 22 ne suka mutu, kamar yadda kakakin ƴan sandan jiyar Tochukwu Ikenga ya bayyana cikin wata sanarwa kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a safiyar Lahadi.
Shaidu sun ce wadanda abin ya shafa sun je ƙarban rabon buhunan shinkafa da wani fitaccen ɗan kasuwa, Ernest Obiejesi, wanda aka fi sani da Obijackson ke rabawa.
Tunibu ya nuna alhininsa
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai Bayo Onanuga ya nuna alhininsa tare da soke duk wasu taruka da ya kamata ya halarta a Legas ranar Asabar.
A fafutukar da ƴan Najeriya ke yi domin samun kayan abinci kyauta, mazauna yankin sun tattake juna, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane.
Cikin wata sanarwa da rundunar ƴan sandan birnin Abuja ta fitar, ta ce cikin waɗanda suka mutu har da ƙananan yara huɗu, yayin da mutane takwas suka samu munanan raunuka, kuma suke karɓar magani a asibiti.
Ƴan sandan sun ce jami'an tsaro sun samu nasarar korar duka mutanen da suka taru a cocin waɗanda ta ce sun fi mutane 1,000.
Tirmutsitsin a Ibadan
Hakan na zuwa ne kwanaki bayan wani turmutsitsin ya kashe ƙananan yara akalla 35 a birnin Ibadan na jihar Oyo, sakamakon wani bikin ƙarshen shekara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI