Cikin ministocin da aka naɗa akwai Bianca Odinaka Odumegu-Ojukwu wadda aka naɗa ta ministar harkokin waje, sai Jumoke Oduwole da aka naɗa ministar masana’antu, kasuwanci da zuba jari.
Sauran sun haɗar da Dr Nentawe Yilwatda ministar jin ƙai, Muhammadu Mai Gari Dingyadi kuwa an naɗa shi ministan ƙwadago da samar da ayyukan yi, sai Idi Mukhtar Maiha ministan ma’aikatar kiwo, sai kuma Yusuf Abdullahi Ata da aka naɗa a matsayin ƙaramin ministan gidaje da ci gaban birane.
Akwai kuma Dr Suwaiba da ta zama sabuwar ministar ilimi, inda kuma aka rage matsayin minista Sunday Dare daga ministan wasanni zuwa mataimakin shugaban ƙasa kan yaɗa labarai da wayar da kai.
Wannan na zuwa ne bayan da Tinubun ya kori ministoci 5 daga kan mukaminsu.
Ministocin da ya kora sun haɗar da Barrister Uju-Ken Ohaneye ministar harkokin mata.
Lola Ade-John, ministar yawon bude bude ido, sai Farfesa Tahir Mamman ministan Ilimi, sai Abdullahi Muhammad Gwarzo ƙaramin ministan Gidaje da ci gaban birane, sai kuma Jamila Bio Ibarhim, ministar matasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI