Tinubu ya karya alƙawarin da muka yi da shin kan farashin fetur - NLC

Tinubu ya karya alƙawarin da muka yi da shin kan farashin fetur - NLC

Mai magana da yawun ƙungiyar NLC, Benson Upah ya bayyana haka a cikin wata hira da ya yi da jaridar Daily Trust da aka wallafa a ƙarshen mako.

Mr. Upah ya bayyana cewa, a lokacin da suka gana da shugaba Tinubu kan batun ƙarin albashin ma'aikata, sai shugaban ya ba su zabi biyu kan ko dai su tsaya a kan naira dubu 65,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi, sannan kuma ba za a ƙara farashin mai ba, ko kuma su zaɓi naira dubu 250,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi amma tare da ƙara farashin litar mai zuwa naira dubu 2,000.

NLC ta bayyana wannan zaɓin da Tinubu ya ba ta a matsayin mai tayar da hankali, amma ƙungiyar ta zaɓi albashin naira dubu 65,000 ba tare da ƙarin farashin litar man fetur ɗin ba domin sauƙaƙa wa talaka raɗaɗin rayuwa.

A halin yanzu dai ƙungiyar ta NLC ta fusata da abin da ta kira " saba yarjejeniyar da ke tsakaninta da shugaban ƙasa" bayan an kara farashin litar mai daga naira 650 zuwa har 1,000.

Shugaban  Najeriya Bola Ahmed Tinubu a China Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a China via REUTERS - GREG BAKER

Kodayake mataimaki na musamman ga shugaba kan yaɗa labarai, Abdulaziz Abdulaziz ya musammanta abin da NLC ta ce, yana mai cewa, babu wata yarjejeniya da ta wakana tsakanin ɓangarorin biyu.

Amma NLC ta dage kan cewa, shi shugaban ƙasa ya san gaskiya domin yana da cikakkiyar masaniya game da wannan alƙawari da suka ƙulla kafin ya karya shi.

Wannan na zuwa ne a yayin da ƴan Najeriya ke ci gaba da kumfar-baƙi kan yadda aka ƙara farashin mai a ƙasar a daidai lokacin da suke tsaka da fama da raɗaɗin janye tallafin man wanda shugaba Tinubu ya yi tun a ranar da aka rantsar da shi.

Janye tallafin man dai ya haddasa tsadar kayayyakin da suka haɗa da abinci da sufuri da ke zama jigo a da'irar tattalin arzikin ƙasa.

Ƙungiyar Kwadagon ta ƙarin farashin litar sam bai yi daidai da tsarin mafi ƙarancin albashin naira dubu 65,000. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)