Tinubu ya kafa kwamitin tabbatar da ƴancin ƙananan hukumomi a ƙasar

Tinubu ya kafa kwamitin tabbatar da ƴancin ƙananan hukumomi a ƙasar

A ranar 11 ga watan Yulin da ya gabata ne kotun ƙoli ta yanke hukuncin baiwa ƙananan hukumomi cikakken ƴancin cin gashin kansu da kuma zare hannun gwamnoni daga tu’ammali da kuɗaɗen su.

Kotun ƙolin ta ce duk wani abu da ya shafi iko ko kuma ƙarfin da suke da shi na tafiyar da aikin ƙananan hukumomi kada gwamnoni su shiga, matakin da bai yi musu dadi ba.

A wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na ofishin sakataren gwamnatin ƙasar Segun Imohiosen ya fitar, ta ce gwamnatin ta amince da wannan kwamiti kuma za’a ba shi duk ƙarfi da gudunmowar da yake buƙata.

A baya dai gwamnonin jihohin ƙasar sun yi kane-kane kan kuɗaɗe da kuma ƙarfin ikon da suke da shi, abinda ya jefa ƙananan hukumomin cikin halin ni ƴasu.

Ana ganin gwamnonin sun ɗauki wannan mataki ne don amfani da talaucin ƙananan hukumomin wajen amfani da su don biyan buƙatar su a siyasance.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)