Tinubu ya gana da Sarkin Ingila a London

Tinubu ya gana da Sarkin Ingila a London

A karo na farko kenan da shugabannin biyu ke ganawa da juna tun bayan wata haɗuwa da suka yi a taron sauyin yanayi na COP 28 a birnin Dubai a bara. 

Mai taimaka wa shugaba Tinubu na musamman a fannin watsa labarai, Bayo Onanuga ya ce, Sarkin Ingilar ne ya gayyaci shugaba Tinubu don ganawa da shi.

Shugabannin biyu sun tattauna kan batutuwan da suka shafi Afrika da duniya, inda suka fi mayar da hankali kan manyan ƙalubalen sauyin yanayi. Inji Onanuga.

Sanarwar Onanuga ta ƙara da cewa, shugabannin biyu sun duba hanyoyin da za su yi aiki tare ƙarƙashin shirye-shiryen taron sauyin yanayi na COP 29 da za a gudanar a Azerbaijan da kuma taron da shugabannin Ƙungiyar Ƙasashe Renon Ingila za su yi a Samoa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)