Gidan rediyon VON ya rawaito ƙaraminin ministan na magana a wani taron mako na Ma'aikatar Ci gaban Matasa a birnin Abuja.
Ministan ya buƙaci ƴan Najeriya da su yi haƙuri da gwamnatin Tinubu, yana mai cewa, nan kusa za a samu kyakkyawan canji ta yadda rayuwar jama'a za ta kyautatu.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba talaka ba ne, shi mai ɗimbin arziki ne, don haka ba za a ce masa yana da burin wawure taskar Najeriya ba. Inji ƙaramin ministan.
Shugaba Tinubu wanda ya yi gwamna har wa'adi biyu a jihar Lagos, sannan ya yi sanata na wani ƙanƙanin lokaci a jamhuriya ta uku, yana da sha'awar harkokin kasuwanci da suka haɗa da ɓangaren yawon buɗe ido da rukunin gidaje da kafofin yaɗa labarai da dai sauransu.
Watakila ƙaraminin ministan matasan na mayar da martani ne ga wasu ƴan Najeriya da ke zargin shugaba Tinubu da kwashe arzikin da Allah ya yi wa ƙasar a daidai lokacin da jama'a ke kokawa kan tsadar rayuwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI