Da ya ke mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mutanen da suke mutu a cikin jirgin, Shugaban ƙasar ya ce, gwamnatin tarayya tana tare da su a wannan lokaci na baƙinciki.
Ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa Bayo Onanuga ya fitar, ta ce shugaban ƙasar ya umarci ƙwararru da su fara aikin binciken nemo sauran mutanen da ba’a gani ba, ko kuma wata shaida game da inda za’a gansu.
Bayanai sun ce jirgin samfurin mai saukar Angulu da kamfanin na NNPC ya haya na dauke da ma’aikata don kaisu wasu gurare don duba aikin da kamfanin keyi lokacin da yayi haɗari kuma ya faɗa gabar teku.
Shugaba Tinubu ta cikin sanarwar ya umarci jami’an bada agaji da sojojin ruwa da su ci gaba da aikin ceto don ganin ko za’a iya gano gawarwaki ko kuma wasu shaidu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI