Tinubu ya buƙaci ƴan Nijeriya su riƙa yi wa shugabanninsu addu'a

A sanarwar da shugaban ya sanyawa hannu da kansa don taya mabiya addinin Kirista murnar bikin Kirsimeti, ya buƙaci ƴan Najeriya su dage wajen yiwa ƙasar da kuma shugabanninsu a dukkan matakai addu’a.

A wannan rana ta Kirsimeti mai cike da farin ciki, ina mika sakon fatan alkairi ga Kiristoci a duk fadin Najeriya da ma duniya baki daya.

A cewarsa, Kirsimeti abu ne da ke nuna cikar anmabta da kawo nasara da ƙaunar juna da salama da kuma haɗin kai.

Shugaba Tinubu ya kuma yi amfani da damar wajen jajantawa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a lokacin turmutsitsin da aka samu kwanan nan a Abuja da Ibadan da kuma Anambra.

Tinubu ya kuma yi addu’ar neman tsari daga sake faruwan hakan a nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)