Tinubu ya bayyana goyon bayansa na samar da halastacciyar ƙasar Falasɗinu

Tinubu ya bayyana goyon bayansa na samar da halastacciyar ƙasar Falasɗinu

Shugaban ya bayyana haka ne a yayin taron ƙungiyar ƙasashen musulmi ta OIC da takwararta ta ƙasashen Larabawa Arab League, da aka gudana a birnin Riyadh fadar gwamnatin Saudiya.

A cikin  wata sanarwa da mai taimaka masa wajen hulda da kafafen yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce shugaba Tinubu na da yakinin cewa samar da halastacciyar ƙasar Falasɗinu ce kadai hanyar kawo ƙarshen rikicin.

Shugaban na Najeriya ya kuma buƙaci ɓangarorin da ke rikici da juya a yankin Gabas ta Tsakiya, su mutunta dokokin kare hakkin dan adam, kamar yadda dokokin ƙasa da ƙasa suka tanada.

Tunda farko a jawabinsa, yarima mai jiran gado na Saudiya Mohammed Bin Salman ya buƙaci tsagaita wuta a hare-hare da Isra’ila ke kaiwa Gaza da Lebanon, tsagaita wutar da jagoran ya kira na wajibi duba da halin da al’ummomin yankunan biyu ke ciki.

Bin Salman ya kuma bukaci bayar da damar shigar da dukkanin kayakin jinkai a Gaza, bisa la'akarin da yadda al'ummar yankin ke cikin mawuyacin hali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)