Tinubu ya bayyana farin cikin dawowar matatar Fatakwal

Tinubu ya bayyana farin cikin dawowar matatar Fatakwal

Sanarwar da Bayo Onanuga ya bayar tace shugaban ya kuma yabawa shugabannin NNPCL saboda jajircewar da suka yi wajen ganin aikin ya gudana duk da kalubalen da akayi ta samu.

Shugaban ya kuma bada umarnin ci gaba da aikin gyaran matatar Fatakwal ta 2 da Warri da kuma Kaduna.

Tinubu ya jaddada aniyar gwamnatinsa na gyara daukacin matatun man kasar domin sun rage wahalhalun da jama'ar kasar ke fuskanta wajen samun tacaccen man da ake bukata a cikin gida la'akari da matsayin Najeriya a matsayin daya daga cikin manyan kasashen dake samar da man fetur a duniya.

Da yake tsokaci akan muhimmancin hakuri da gaskiya da kuma jajircewa wajen sake gina manyan kadarorin kasar, shugaba Tinubu ya yi kira ga jama'a da hukumomin da aka dorawa alhakin kula da irin wadannan kadarori da su mayar da hankali wajen kula da amanar da aka ba su.

Shugaban ya kuma sake tabbatar da matsayin gwamnatinsa na tabbatar da dogaro da kai a bangaren makamashi da kuma inganta bangaren fita da shi domin samun kudaden shiga.

Matatar man Fatakwal Matatar man Fatakwal © Nigeria Presidency

Bayan kwashe dogon lokaci ana saran fara aikin matatar man kuma ana dagewa, a yau matatar ta fara aiki gadan gadan, matakin da ake ganin zai taimaka gaya wajen samarwa kasar tacaccen man da ake bukata tare da wasu nau'oin kayayykin da ake bukata wajen sarrafa takin zamani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)