Tinubu ya amince da ƙarin kaso 300 kan albashin ma'aikatan ɓangaren shari'a

Tinubu ya amince da ƙarin kaso 300 kan albashin ma'aikatan ɓangaren shari'a

 

Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mataimakin shugaban ƙasar kan harkokin majalisar dokoki Bashir Garba Lado.

Idan za’a iya tunawa majalisar dokokin Najeriya ta amince da dokar wadda ta buƙaci shugaban ƙasar da ya amince da ƙarin albashin wanda ya kamata ya fara tun watan Yunin da ya gabata.

Ta cikin sanarwar, Garba Lado ya kwatanta rattaba hannu kan dokar a matsayin wani ci gaba na musamman da shugaban ya kawo, wanda zai ƙarfafa ɓangaren shari’ar ƙasar da kuma taimakwa wajen rage cin hanci da ke farwua a ɓangaren.

Yayin rattaba hannu kan sabuwar dokar, shugaban ƙasar ya buƙaci ɓangaren shari’ar da su ƙara ƙaimi wajen aikin su da kuma tabbatar da adalci don samun zaman lafiya da kuma ƙwarin gwiwa ga bangaren shari’a daga ƴan kasa.

Wannan na zuwa ne ƙasa da wata guda bayan da shugaban ya amince da naira dubu 70 a matsayin mafi ƙarancin albashin ma’aikata, matakin da ya zo bayan murza gashin baki tsakanin ɓangaren gwamnati da na ƴan kwadago.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)