Tinubu na murna da rahotan ci gaban tattalin arziki

Tinubu na murna da rahotan ci gaban tattalin arziki

Mai magana da yawun shugaban Sunday Dare ya ce shugaban Tinubu ya yaba da matakin tare da jaddada matsayin gwamnatinsa na ganin ta bunkasa tattalin arzikin kasar zuwa dala triliyan guda nan da shekarar 2030.

Rahotan hukumar NBS ya bayyana cewar an samu ci gaban ne a bangarorin noma da sufuri da ilimi da bangaren lafiya da gidaje da inshora da man fetur da kuma masana'antu. Tinubu ya ce ba zai gaza ba har sai ya ga 'yan Najeriya sun samu sauyi a cikin aljihunsu tare da kuma inganta rayuwarsu.

Sai dai masana da 'yan Najeriya na bayyana cewar wadanann alkaluma ya zuwa yanzu a takarda suke, domin bai kai ga taba rayuwar jama'a ba lura da irin kuncin rayuwar da ake fuskanta a cikin kasa.

Dakta Kasum Kurfi, masanin tatatlin arziki yace tabbas akwai wasu alamu na samun karin kudade da gwamnati ke yi ta bangaren man fetur da noma da masana'antu, amma kuma rayuwar jama'ar kasar har yanzu basu inganta ba lura da yadda kayan abinci ke tsada da yadda talauci ya yiwa jama'a katutu.

Masanin ya ce akasarin fuskokin 'yan Najeriya a turmuke suke saboda kuncin rayuwa, yayin da babu wani rahotan ci gaba na samar da ayyukan yi kamar yadda kasashen da suka ci gaba ke auna mizanin bunkasar tattalin arziki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)