Idan dai ba a manta ba, a farkon makon da ya gabata ne aka samu ambaliyar ruwa a jihar, wacce ta shafe sama da kaso 70 a birnin Maiduguri, lamarin da ya hukumomi suka bayyana a matsayin annoba mafi muni da aka samu a birnin cikin gwamman shekaru.
Sa’aoi bayan faruwar lamarin ne dai mataimakin shugaban Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar Sanata Kashim Shettima, ya isa birnin don jajantawa al’umma da gwamnatin jihar.
A cewar gwamnan jihar Babagana Umara Zulum, kimanin mutane miliyan biyu ne iftila’in ya shafa, inda daruruwan mutane suka bar gidajensu.
Tuni dai gwamnatoci da ƙungiyoyi masu zaman kansu da kuma dai-daikun jama’a suke tashi tsaye wajen tallafawa waɗanda lamarin ya shafe, ganin yadda mutane ke cikin matukar buƙatar agajin gaggawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI