Tinubu da iyalansa na neman kassara Najeriya - Atiku Abubakar

Tinubu da iyalansa na neman kassara Najeriya - Atiku Abubakar

Cikin wata sanarwar da mai bai wa Atiuku shawara a kan harkokin yada labarai Paul Ibe ya rabawa manema labarai ta ce, irin illar da Tinubu ya yi wa Najeriya, ko da ya bar mulki, gyaran shi zai yi matukar wahala.

Atikun ya zargi shugaban ƙasar da hada mulkin da ya ke jagoranci da harkokin shi na kasuwanci, kamar yadda wani kamfaninsa a Lagos ke ƙarɓar kuɗaɗen harajin gwamnati da ake kira Alpha Beta, yanzu haka ya fara aikata haka a matakin gwamnatin tarayya.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana takaicinsa a kan yadda shugaban kasar ya mayar da wani sashe na kamfanin man NNPC ƙarkashin kamfanin ɗan uwansa Wale Tinubu na Oando.

Ƙokarin sayen jarin NNPC

Atiku ya bayyana damuwarsa a kan sake shirin sayar da kamfanin NNPC domin ba shi damar sake saye hannayen jarinsa, inda ya bayyana shi a matsayin wani yunkurin mamaye kamfanin da wasu fitattun mutanen dake kusa da shugaban kasar ke shiryawa.

Tsohon shugaban ƙasar ya ce a watan Oktobar shekarar 2022, watanni 5 kafin zaɓe, kamfanin NNPC ya sanar da kulla yarjejeniyar da Oando domin ƙarbe gidajen man sa, duk da cewa NNPC na da gidajen mai 550 a sassan ƙasar, yayin da Oando ke da 94 kacal.

Ci gaba da rike Mele Kyari a NNPC

Atiku ya ce wannan yarjejeniyar ce ta sanya shugaban ƙasar sake bai wa shugaban NNPC Mele Kyari sabon wa'adi duk da rashin kwarewarsa, yayin da shugaban ƙasar ya kuma nada tsohon mai gidansa a kamfanin Mobil, Pius Akinyelure a matsayin shugaban majalisar gudanarwar NNPC, yayin da shi kuma ya rike mukamin ministan mai.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce gwamnatin Najeriya ta biya Wale Tinubu makuɗan kuɗaɗe kafin karɓar gidajen man sa, matakin da ya bayyana shi a matsayin haramcacce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)