Tchiani ya rushe hukumar yaƙi da cin hanci da ya kafa bayan bandaƙaɗo badaƙala

Tchiani ya rushe hukumar yaƙi da cin hanci da ya kafa bayan bandaƙaɗo badaƙala

Tun bayan ƙwace mulki daga gwamnatin farar hula da shugaban mulkin soji Abdurrahman Tchiani ya yi ne ya sanar da kafa wata hukuma ta yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar mai suna COLDEF.

Wannan na zuwa bayan ministan harkokin cikin gida a Jamhuriyar Nijar Mohammed Tumba ya bayyana cewa bayan wani bincike da aka gudanar, an bankaɗo yadda aka yi wata almundahana da rub da ciki da dukiyar jama'a a cikin kananan hukumomin kasar Niger.

A wata hira da aka yi da ministan harkokin wajen a gidan talabijin na kasar, ya ce an yi ɓarna a ƙananan hukumomi da dama, a da'irar birnin Damagaram ne lamarin ya fi muni, inda sama da milyan 355 na kuɗin ƙasar suka salwanta, lamarin da ya harzuka masu yaki da cin hanci da rashawa da ƴan rajin kare demokaradiyya a ƙasar.

A kadan daga cikin ɓarnar da aka tafka a kananan hukumomin da ministan Janar Mohamed Tumba ya nuna, ya ce takardunsu sun iso gareshi ne inda suka nuna sama da milyan dubu ne ya salwanta.

Ita dai wannan hukuma an ɗorawa mata alhakin kwato dukiyoyin da wasu suka mallaka ba bisa ka'ida ba.

Hukumar yaki da rashawar ta Jamhuriyar Nijar da gwamnatin soji ta kafa ta kunshi sojoji da ƴan sanda da alƙalai da  ma ƙungiyoyin fararen hula.

Wasu sabbin rahotanni na baya-bayannan ne dai suka banƙado cewar an samu badaƙalar cin hanci ƙarƙashin hukumar da gwamnatin mulkin soji ta kafa, abin da ake ganin shine dalilin rushe ta.

A gefe guda kuma al’ummar Jamhuriyar Nijar da dama ba su gamsu da yadda hukumar ke tafiyar ayyukanta ba na yaki da cin hanci da ma batun kuɗin da yan kasar suka sata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)