Tattalin arziƙin Najeriya ya sake haɓaka mafi ƙololuwa a shekaru 3- NBS

Tattalin arziƙin Najeriya ya sake haɓaka mafi ƙololuwa a shekaru 3- NBS

Alƙaluman sun ce ƙarfin tattalin arziƙin ƙasar a ma’aunin GDP ya tsaya a maki 3.84 fiye da maki 3.46 da aka gani a watanni 4 na rukuni na 3 duk dai a cikin shekarar ta 2024.

A cewar NBS haɓakar tattalin arziƙin na da nasaba da bunƙasar ɓangarorin samun kuɗaɗen shigar gwamnati da ya ƙaru da kashi 5.37 daga kashi 3.40 a baya da kuma kashi 2.74 a 2023.

Duk da cewa tattalin arziƙin na Najeriya ya haɓaka amma bayanai sun ce matakin da ya ke a yanzu ya yi ƙasa da alwashin da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya ɗauka lokacin da ya karɓi ragamar ƙasar mafi yawan jama’a a tsakiyar shekarar 2023.

Farfaɗowar tattalin arziƙin a cewar Bankin Duniya na da nasaba da matakan tsuke bakin aljihu da kuma manufofin shugaba Tinubu ciki har da harajin da ya ke ci gaba da sanyawa ga ɓangarori da dama.

Sai dai duk da farfaɗowar tattalin arziƙin na Najeriya al’ummar ƙasar na ci gaba da faɗawa a matsi da tsadar rayuwa ta kowacce fuska, yayinda darajar kuɗin ƙasar ke ci gaba da lalacewa.

Haka zalika yunwa na ci gaba da zama babbar barazana ga al'ummar wannan ƙasa mafi yawan jama'a a nahiyar Afrika a wani yanayi da Talakawa ke ci gaba da talaucewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)