Shugaba Bola Tinubu ya sanar da janye tallafi ne jim kadan bayan da aka rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun shekarar da ta gabata, lamarin da ya kai ga ƙarin farashin mai da sama da kashi ɗari 3.
A wata ganawa da jaridar tattalin arziki ta Finacial Times, Obasanjo ya caccaki yadda Tinubu ya janye tallafin mai ba tare da shimfida wani tsari ba.
Wannan bayani na Obaasanjo ya yi hannun riga da matakin Tinubu na janye tallafi, dyba da cewa gwamnatinsa na ci gaba da ikirarin babu tallafi a halin da ake ciki.
Obasanjo ya ce akwai abubuwa da dama da ya kamataa a yi la’akari da su kafin janye tallafi, ba wai kawai a tashi rana tsaka a ɗauki matakin da zai zame wa al’umma sharri ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI