Talakawan Najeriya miliyan 13 za su ƙara tsiyacewa a 2025 - Rahoto

Talakawan Najeriya miliyan 13 za su ƙara tsiyacewa a 2025 - Rahoto

Cikin rahoton wanda PwC ta fitar bayan nazartar ƙunshin kasafin kuɗin Najeriya na 2025 ya nuna cewa a shekarar da muke ciki ƴan Najeriya miliyan 13 ko fiye na gab da ƙetare layin da mahukuntan ƙasar suka shata da nuna cewa duk wanda ya kai layin kai tsaye yana cikin matsanancin talaucin.

A cewar rahoton mutanen miliyan 3 tun tuni na sahun matalauta amma a shekarar da muke ciki za su ƙara tsiyacewa sakamakon matakan mahukuntan ƙasar kama daga karya darajar naira da kuma kara kudin ruwa baya ga ƙara haraji wanda ya haddasa hauhawar farashi da tsadar rayuwa.

Rahoton na PwC ƙungiyar da ke bibiyar tattalin arziƙin ƙasashe da kuma ƙarfin aljihun al’umma na zuwa ne bayan alƙaluman da hukumar ƙididdiga ta Najeriyar NBS ta fitar da ke nuna cewa hauhawar farashi ya kai matakin maki 34.80 cikin watan Disamban bara.

Bugu da ƙari duk dai cikin makon nan, shugaban ƙungiyar masu masana’antu ta Najeriya Francis Meshioye ya bayyana yadda suka tafka asara sakamakon yadda ƴan ƙasar suka ƙauracewa saye-saye lamarin da kai tsaye PwC ke alaƙantawa da tsadar rayuwa da kuma matsanancin talaucin da al’ummar Najeriyar ke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)