Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, Olarenwaju Ishola, a wajen taron ya kuma baiwa mazauna Legas tabbacin kasancewar ‘yan sanda a yayin gudanar da zanga-zangar, inda ya ce manufarsu ita ce tabbatar da tsaro da zaman lafiya.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu © Nigeria PresidencyDaya daga cikin wadanda suka shirya taron kuma shugaban sashen yakin neman hakkin ilimi na kasa Hassan Soweto, wanda ke cikin taron, ya kuma tabbatar da tabbacin kwamishina na hadin gwiwa da masu zanga-zangar.
A wajen taron, wanda aka gudanar a cibiyar ‘yan jarida ta kasa da kasa dake unguwar Ogba a Legas, ‘yan biyun sun bayyana dalilan da ya kamata a gudanar da zanga-zangar a watan Oktoba, inda suka ce baya ga tsadar man fetur, ana zargin gwamnatin shugaba Bola Tinubu da daukar matakan tsuke bakin aljihu.
Wasu mata kena da ke zanga-zangar neman kare hakkokinsu. AP - Sunday AlambaMasu shirya zanga-zangar sun bukaci ‘yan Legas da su kasance tare da su don nuna rashin gamsuwarsu da shirye-shirye da manufofin gwamnati mai ci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI