Rahotanni daga jihar Legas da ke kudancin Najeriya,wani magidanci mai suna Emmanuel Bolaji ganin halin kutsi da ake rayuwa a ciki ,ba shi da wani zabi: ya kori direban sa, ya kuma mayar da motarsa kirar Honda Pilot, zuwa wurin ajiye motoci.
Kamar Emmanuel Bolaji mai shekaru 72 tsohon ma’aikaci ne a harkar lafiya,wanda kuma ke ritaya, da yawa daga cikin ‘yan Najeriya,ciki har da na masu matsakaicin matsayi, sun fara yin watsi da motocinsu, saboda tsadar man fetur.
Matatar man Dangote a Lagos REUTERS - Temilade AdelajaEmmanuel Bolaji ya kara sa da cewa “ba ni da halin biyan kuɗin mai, don haka na ajiye motata a gida,yanzu kam ina amfani da motocin sufuri na jama’a wajen gudanar da ayuka.
Tun hawansa karagar mulki a watan Mayun 2023, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki da nufin janyo hankalin masu zuba jari daga kasashen waje da kuma cike gibin kudaden gwamnati.
Yadda wasu masu motoci ke bin layin mai a Najeriya. REUTERS - Afolabi SotundeDaga cikin matakan da ya kamata a dauka, kawar da tallafin mai, wanda tsawon shekaru da dama ya taimaka wajen rage farashin man fetur.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI