Sokoto ta kaddamar da shirin inganta karatun yara mata

Sokoto ta kaddamar da shirin inganta karatun yara mata

A karkashin wannan shiri da aka yiwa suna AGILE kowanne shugaban makaranta zai dinga karbar naira 200,000 kowanne wata wanda zai dinga amfani da su wajen gudanar da wasu kananan aikace aikacen da suka shafi ci gaban karatun makarantarsa.

Gwamnan jihar Ahmad Aliyu ya jaddada cewar shirin bada ilimi ga jama'ar jihar na daga cikin manyan manufofin gwamnatinsa, kuma za su ci gaba da tallafawa makarantun jihar baki daya.

Wasu daga cikin shugabannin sakandaren Sokoto da takardar kudin da suka karba Wasu daga cikin shugabannin sakandaren Sokoto da takardar kudin da suka karba © Sokoto Government

Aliyu ya bukaci shugabannin makarantun sakandaren dake jihar da su dada jajircewa wajen ganin sun sauke nauyin dake kan su tare da gargadin cewar duk wanda aka samu ya karkata wanann tallafi zai gamu da fushin hukuma.

Gwamnan ya bayyana cewar a shirye gwamnati mai ci take ta bai wa 'yaran jihar Sokoto ilimin da ta dace da su domin gogagyya da takwarorinsu na Najeriya baki daya.

Jihar Sokoto na daga cikin jihohin da ke kokari wajen ganin sun inganta karatun yara mata a arewacin Najeriya ganin irin matsalolin da ake fuskanta a yankunan karkara da kuma matsalar tsaron da ta addabi yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)