
Mai taimakawa gwamnan jihar ta Kebbi wajen hulɗa da kafafen yada labarai Abudullahi Idris Zuru ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce jami’an sojojin Najeriya sun samu nasarar lalata maɓoyar ƴan ta’addan, tare da kwato shanu da dama da suka sace, bayan da suka tsere suka barsu.
A cewarsa, wannan nasara dai ta biyo bayan neman ɗauki daga gwamnatin tarayyar ƙasar da gwamnan jihar Dr Nasir Idris ya yi, don kare jama’ar jihar daga barazanar da suke fuskanta daga wajen ƴan ta’addan.
Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu, ya bada tabbacin cewa za su fatattaki ƴan ta’addan na Lakurawa da ke addabar shiyar Arewa maso yammacin ƙasar.
Za mu fatattaki wadannan Lukarawa daga ƙasarmu, ƴan Boko Haram da suka addabi ƙasarmu, yanzu sun gudu suna tafiya wasu ƙasashe makwabta saboda a yanzu ba zasu iya gudanar da ayyukansu a Najeriya ba.
Ƴaƴan ƙungiyar ta Lakurawa, sun janye ne dai bayan da jami’an sojin Najeriya da suka hada da na ƙasa da kuma na sama suka kai musu hare-hare maɓoyarsu a jihohin Kebbi da Sokoto.
Wannan kuwa ya biyo bayan harin da Lakurawan suka kai garin Mera da ke yankin Ƙaramar Hukumar Augie na jihar Kebbi, da yayi sanadiyar mutuwar mutane 11.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI