Sojojin Najeriya sun kashe mataimakin Bello Turji da wasu kwamandoji

Sojojin Najeriya sun kashe mataimakin Bello Turji da wasu kwamandoji

 

Manjo Janar Edward Buba Kakakin rundunar sojin Najeriya ya ce an kashe mataimakin Bello Turji, Aminu Kanawa a wani samame da aka gudanar a ranakun Litinin da Talata. A wata sanarwa da ya fitar a jiya Laraba, Manjo Janar Buba, ya ce an kashe wasu ‘yan ta’adda 24 a samamen.

Kakakin rundunar sojin Najeriya ya ce an kaddamar da ayyukan ne a sansanonin Bello Turji da ke jihohin Sakkwato da Zamfara, tsakanin Litinin zuwa Talata.

Kakakin ya ce an kashe wasu manyan kwamandojin Bello Turji da suka hada da Abu Dan Shehu, Jabbi Dogo, Dan Kane, Basiru Yellow, Kabiru Gebe, Bello Buba, da Dan Inna Kahon-Saniya-Yafi-Bahaushe, a cikin ayyukan.

Ya ce sojojin sun kuma raunata wasu makusantan Bello Turji da suka hada da Dosso (kanin Turji) da Danbokolo (daya daga cikin makusantan Turji).

“Bugu da kari, sojoji sun kashe ‘yan ta’adda sama da 24 da suka tsere daga sansanin Turji da ke kusa da kananan hukumomin Gebe da Isa a jihar Sakkwato, da kuma kewayen Gidan Rijiya a karamar hukumar Shinkafi ta Zamfara. “Sojoji sun kuma kashe wani fitaccen dan ta’adda a yayin harin da aka kai a yankin Turji da ke kusa da babban filin Fakai.

“An bayyana shi da Suleiman kuma (mai biyayya ne ga fitaccen shugaban ‘yan ta’adda, Halilu Sububu). “Marigayi Suleiman ya jagoranci tawagar da za ta taimaka wajen ceto sansanin Bello Turji, wanda ya ruguje lokacin da aka kawar da shi a lokacin.

Manjo Janar Buba ya ce mutuwar babban hadiminsa na biyu, na kusa da Turji, kwamandoji da kuma masu fada a ji, babbar illa ce ga tsarin sadarwarsa a yankin arewa maso yammacin Najeriya, inda yake gudanar da ayyukansa. Ya ce kungiyar ta Turji ce ke da alhakin sace-sace da ta’addanci da dama a shiyyar, musamman a kananan hukumomin Zurmi, Shinkafi, Isa, da Sabon Birni na jihohin Zamfara da Sokoto.

 “Gaba ɗaya, sojoji ba sa ja da baya har sai an halaka waɗannan ‘yan ta’adda gaba ɗaya a cewar Manjo Janar Buba.

 Ya kara da cewa, "Ayyukan dakaru na da nufin samar da yanayi na aminci da tsaro ga dukkan 'yan kasar." Duk da nasarorin da sojoji ke samu a kan 'yan ta'adda a arewa maso yammacin Najeriya, Bello Turji ya ci gaba da gujewa sojojin. Hare-haren da ya kai kan al'umomin yankin arewa maso yammacin Najeriya ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane a 'yan shekarun nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)