
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi ya fitar, ta ce sun samu nasarar ce a jerin wasu hare-hare da suka kai wa ƴan ta'addan, daga tsakanin ranar 1 zuwa 10 ga wannan watan.
Sanarwar ta ce daga cikin manyan ƴan ta’addan da ta samu nasarar kashewa sun haɗa da Kachalla Na Faransa da Dogon Bakkwalo da Auta Gobaje sai kuma Dan Mai Dutsi, sannan kuma sun samu nasarar lalata maɓoyarsu a yankunan ƙananan hukumomin Shinkafi da kuma Zurmi.
Sojojin sun kuma samu nasarar kwato makamai da alburusai da kuma kuɓutar da dama daga cikin mutanen da ƴan bindigar suka yi garkuwa da su.
Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi ya kuma jaddada aniyar rundunar ta Operation Fansan Yamma, na yaƙi da ƴan ta’adda a shiyar Arewa maso Yamma da kuma jihar Neja, inda ya ce akwai buƙatar al’umma su basu bayanan inda maɓoyar kasurgumin ɗan bindigar nan Bello Turji ya ke don kawo ƙarshensa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI