Danjuma ya bukaci manyan hafsoshin da su tashi tsaye wajen murkushe 'yan bindiga da kuma dawo da Najeriya a kan tafarkin zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali.
Tsohon ministan ya ce shugabannin sojojin ba su da wani uzuri da za su gabatarwa jama'a dangane da ci gaba da kisan da kuma garkuwa da mutane.
Janar Danjuma ya ce babbar matsalar Najeriya a yau itace ta tsaro, kuma ya zama wajibi a kawo karshen ta, ya yin da ya ke shaidawa hafsoshin tsaron cewar a wannan lokaci babu wani dalili da za su gabatar wanda jama'a za su amince da shi na gazawa daga wurin su.
Babban hafsan tsaron kasa Janar Christopher Musa ya amince da cewar sojojin kasar na cikin yanayin da ake bukata na dawo da zaman lafiyar da ake bukata duk da wasu kalubalen da suke fuskanta.
Janar Musa ya ce suna iya bakin kokarin su kuma ba za su yi kasa a gwuiwa wajen ganin wannan matsalar 'yan bindiga ta ci gaba ba tare da samun nasara a kan ta ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI